Halin ni-ya su da fursunoni suke fuskanta daga mayakan kungiyar Rapid Support Forces ta Dakarun kai daukin gaggawa ta Sudan a gidajen yari
Gidan talabijin na Aljezeera ta watsa rahoton cewa: Daya daga cikin wadanda mayakan Rapid Support Forces ta Dakarun kai daukin gaggawa suka kama tare da garkame shi a gidan kurkuku mai suna Tariq Abdullah ya bayyana cewa: Bayan kama shi da abokansa an kai su gidan yarin Soba da ke kudu maso gabashin birnin Khartoum fadar mulkin kasar, inda suka ga ana fitar da gawarwakin mutane 12 daga gidan kurkukun, kuma sun mutu ne sakamakon kishin ruwa da yunwa, kamar yadda akasarin fursunoni a gidan yarin sun mutu ne saboda rashin abinci mai gina jiki da kuma rashin ingancin wurin sakamakon cinkoson gidan yarin.
Tariq, babban editan jarida ne na Al-Ahram Al-Youm, ya ce: Wadanda aka tsare da su, bayan sun mutu ana sanya gawarwakinsu ne a cikin jakunkuna wadanda aka kebe don wadanda suka mutu a annobar Corona, sannan a sanya su a cikin kwalaye buɗaɗɗu, inda ake daukansu zuwa wasu wurare da ba a san ko ina ne ba, tare da rakiyar yan tsirarun kungiyar ta Rapid Support Forces.