Mai ba da shawara ga jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Kalamai masu karo da juna na Trump da mataimakansa sun zubar da kwarin gwiwa ga gwamnatin Amurka
Mai bai wa Jagoran juyin juya halin Musulunci shawara ya bayyana cewa: Sabani da ake ci gaba da yi a cikin maganganu da ayyukan Trump da takwarorinsa na haifar da rashin amincewa da gaskiyar gwamnatin Amurka.
Ali Akbar Velayati mashawarcin Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya yi tsokaci a cikin wani sako da ya wallafa a dandalin X kan kalamai masu cin karo da juna da jami’an Amurka suka yi.
Mai bai wa Jagoran juyin juya halin Musulunci shawara ya ce ci gaba da cin karo da juna a cikin maganganu da ayyukan Trump da mukarrabansa ya haifar da rashin amincewa da gaskata gwamnatin Amurka.
Velayati ya kara da cewa: Wannan batu ba a taba ganin irinsa ba a tarihin diflomasiyya a duniya kuma yana nuni da halin da ake ciki a cikin gwamnatin Amurka.