Wata ‘Yar Jarida Ta Nuna Mamaki Kan Nuna Damuwa Da Ciwon Biden Maimakon Kisan Gillar ‘Yan Sahayoniyya

A lokacin da kasashen Yamma suka yi biris da kisan gillar da ake yi a Gaza, kuma suna kuka kan cutar da tsohon shugaban Amurka

A lokacin da kasashen Yamma suka yi biris da kisan gillar da ake yi a Gaza, kuma suna kuka kan cutar da tsohon shugaban Amurka Biden ke fama ita

Marubuciya kuma ‘yar jarida kasar Autraliya Caitlin Jahnstone a cikin wani makala da ta rubuta ta siffanta abin da ta kira matsayin munafuncin ƙasashen yamma wajen mu’amala da kimar ɗan adamtaka da gwada alhini kan batun ciwon tsohon shugaban Amurka Joe Biden game da cutar sankara da ke fama da ita a matsayin mafarin fallasa sabanin da ke cikin maganganun siyasa da kyawawan ɗabi’u na Amurka dangane da laifukan yaƙi musamman abin da ke faruwa a Gaza.

Tana cewa: Ciwon daji na Prostate yana da ‘yancin wanzuwa. Yayin da ciwon daji na Biden yana da ‘yancin kare kansa.” Johnstone ta yi izgili game da “tausayin Biden” da wasu kafofin watsa labaru na yammacin Turai da da’irori na siyasa suka nuna, tana mai sukar bacin ran da alhini da aka yi na kalamai “marasa dacewa” game da rashin lafiyar Biden, yayin da ya yi watsi da ainihin fushin dubban wadanda suka fadi sakamakon yanke shawarar siyasarsa, musamman a cikin mahallin cikakken goyon bayan Amurka ga gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila wajen aiwatar da kisan gilla kan Falasdinawa a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments