Wata Kotun A Murka Ta Haramtawa HKI Kafa Na’urorin Leken Asiri A Wayoyi Masu WattsApp

Wata kotu a Amurka ta yanke hukuncin hana kamfanen samar da kayakin leken asiri na HKI NSO kakkafa na’urar leken asiri a kamfanin sadarwa ta

Wata kotu a Amurka ta yanke hukuncin hana kamfanen samar da kayakin leken asiri na HKI NSO kakkafa na’urar leken asiri a kamfanin sadarwa ta WattsApp saboda ayyukan leken asiri.

Kamfanin dillancin labaran Ip na kasar Iran ya nakalto mai sharia Phyllis Hamilton na cewa kamfanin NSO ya kakkafa na’urarsa ta leken asiri  Pegasus kan wayoyin mutane kimani 1,400 in da na’urar yake kunna camera dau daukar hotuna na mutane, da sauti ko kuma ya shiga ya dauki sakonni masu muhimmanci a cikin wayoyunsu ba tare da sun sani ba.

Amma Hamilton bata amince da taran dalar Amurka miliyon  $168  wanda kamfani Meta ta bukata ba.

Na’uran leken asiri na Pegasus dai ana tsarashi ne a HKI kuma kamar yadda bayanai suka zo, HKI tana sayarwa gwamnatoci ne don su yi aikin leken asiri ga wasu mutanen da take tuhumarsu da aikata wasu laifuka don samun bayanai danagane da su ta wayoyinsu. Ko kuma tamanhajojin sadarwa na WattsApp da meta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments