Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka da harshen larabci ta yi murabus saboda rashin amincewarsa da siyasar fadar white House akan yakin Gaza.
Halah Garidh wacce take Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka, da harshen larabaci, ta sauka daga kan mukamin nata ne dai saboda rashin amincewa da siyasar shugaban kasar Joe Biden akan yakin Gaza.
Watanni bakwai sun shude daga lokacin da HKI ta shelanta yaki akan Gaza da mutanenta, amma har yanzu Amurka tana cigaba da aike wa da HKi makaman da take amfani da su wajen kashe Paalsdinawa.
Dama gabanin wannan lokacin wasu jami’an gwamnatin Amurka su uku sun sauka daga kan mukamansu saboda kin amincewa da siyasar gwamnatin kasar wajen taimakawa HKI da makamai da kuma kudade,domin cigaba da yi wa mutanen Gaza kisan kiyashi. Daga cikinsu da akwai Anil Shiling, ta jam’iyyar Democrat, sai kuma Tarik Habash, wanda mataimakin shugaban kasar Amurka ne na musamman a ma’aikatar ilimi. Haka nan kuma Josh Paul wanda jami’in siyasa da sojan ne a ma’aikatar harkokin waje.