Search
Close this search box.

Iran: Ana Ci Gaba Da Kokarin Ganin An Kawo Karshen Kisan Kiyashi A Gaza

Ministan harkokin wajen kasar Iran Amir Hussain Abdullahiyan ya bayyana cewa za’a fara wani sabon kokari daga yankin gabas ta tsakiya da kuma sauran kasashen

Ministan harkokin wajen kasar Iran Amir Hussain Abdullahiyan ya bayyana cewa za’a fara wani sabon kokari daga yankin gabas ta tsakiya da kuma sauran kasashen duniya don tabbatar da cewa an dakatar da kissan kiyashi a gaza.

Kamfanin dillancin labaran IRAN-PARS ya nakalto ministan yana fadar haka a safiyar yau litinin ya kuma kara da cewa, gwamnatin kasar Amuraka da kuma ta Benjamin Natanyahu ne suka durkusar da kokarin da aka yi ta yin a kawo karshen yakin na gasa.

Ya ce tallafin da gwamnatin Amurka take bawa HKI na daga cikin abubuwan da suka hana kawo karshen kisan kiyashi a Gaza, da kuma bushewar zuciyar firai ministan HKI wanda ya dage kan ci gaba da yaki a gaza duk tare da kiraye kirayen kasashen duniya na kawo karshen yakin.

Labarin ya kara da cewa, ma’aikatar kiwon lafiya ta zirin gaza ta bada sanarwan shahadar Falasdinawa akalla 34,000 mafi yawansu mata da yara, a yayinda wasu 78 000 suka ji rauni.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments