Shugaban kasar Chain Xi Jenpeng wanda yake ziyarar aiki a kasar Faransa ya bayyana cewa yakin gaza ya girgiza zukatan mutane da dama a kasashen duniya.
Kamfanin dillancin labaran Chinhuwa na kasar Chiana ya nakalto shugaban yana fadar haka a lokacinda yake jawabi gay an jaridu, ya kuma kara da cewa rashin aiwatar da kudurorin MDD a rikicin kudancin Asiya shi yasa al-amarin ya kai inda ya kai a halin yanzu.
Ya kara da cewa rashin aiwatar da wadannan kudurori na MDD ya karkatar da rikicin kudancin Asia zuwa yaki a gaza, kuma hanyar warware matsalar ita ce aiwatar da kudurorin MDD kan rikicin.
A wani bangare na jawabinsa shugaba Xi ya bayyana cewa kasar Faransa da Chaina suna tarayya a kan wasu al-amura da suka shafi rikicin falasdinawa da HKI, kuma dole ne kasashen biyu su yi aiki tare don warware matsalolin da suka hana ruwa gudu a cikin rikicin.