Search
Close this search box.

Iran Zata Yada Fasahar Nukliya Ta Zaman Lafiya A Tatsakanin Kasashen Duniya

Shugaban hukumar makamashin nukliya na kasar Iran Muhammad Islami ya bayyana cewa hukumarsa tana da shirin yada fasahar makamashin nukliya ga kasashen duniya. Kamfanin dillancin

Shugaban hukumar makamashin nukliya na kasar Iran Muhammad Islami ya bayyana cewa hukumarsa tana da shirin yada fasahar makamashin nukliya ga kasashen duniya.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Islami yana fadar haka a taron kasa da kasa ta makamashin nukliya wanda aka  bude a birnin Esfahan na kasar Iran a yau Litinin.

Ya kuma kara da cewa kasar Iran tana da shirin gina cibiyoyin samar da wutan lantarki tare da amfani da makamashin nukliya har 20 nan da shekara ta 2040 miladiyya. Kuma mafi yawansu zasu kasance ne a bakin ruwan tekun Farisa daga kudanci da kuma tekun Caspian daga arewacin kasar.

Islami ya kamala da cewa wannan gagarumin aikin yana bukatar kudade da kuma zuba jari ko daga ciki ko kuma wajen kasar. Don haka a halin yanzu gwamnatin kasar ta fara shirye shiryen ganin inda zata samar da kudaden gina wadannan cibiyoyi. Sannan yace nan da shekaru biyu za’a kafa makarantar koyon fasahar nukliya a birnin Esfahan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments