Ayarin wanda aka bai wa sunan: “Jajurcewa” zai tashi ne daga Tunisiya jim kadan bayan da sojojin HKI su ka hana wani jirgin ruwan dake dauke da masu fafutuka daga kasashen turai,isa gabar ruwan Gaza.
Ayarin na ” Jajurcewa’ zai bi ta ruwan Libiya, sannan Masar daga can kuma ya nufi gabar ruwan Gaza.
Ayarin yana dauke da masu fafutuka 7,000 daga kasashen Tunisiya, Moroko, Aljariya, Murtaniya, da Libiya.
Kwamitin kasa da kasa domin karya killace Gaza, wanda ya shirya wannan tafiyar, ya kuma yi wani kiran ga ‘yan fafutuka a duniya da su shirya wasu tafiye-tafiyen ta ruwa zuwa Gaza, domin kawo karshen killace yankin da aka yi tun 2007.