Wani Tsohon Ma’aikacin MDD Ya Yi Kira Ga Amurkawa Su Dawo Daga Rakiyar Gwamnatin Amurka Da Natanyahu

Tshohon daractan hukumar kare hakkin bil’ada ta MDD Craig Mokhiber ya yi kira ga Amurkawa su dawo daga rakiyar gwamnatin Trump da kuma firai ministan

Tshohon daractan hukumar kare hakkin bil’ada ta MDD Craig Mokhiber ya yi kira ga Amurkawa su dawo daga rakiyar gwamnatin Trump da kuma firai ministan HKI Benyamin Natanyahu, mashayin jinin Falasdiwa, a dai dai lokacinda yake ziyararsa ta farko zuwa kasar Amurka tun bayan da Trump ya sake dawowa fadar White House.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Craig Mokhiber ya na fadar haka a shafinsa na X a jiya litinin, ya kuma kara da cewa, irin tarban da gwamnatin Trump ta bawa Natanyahu, da kuma yadda wasu yan majalisar dokokin kasar suka himmatu, ya nuna cewa babu bambanci a tsakanin gwamnatin Joe Biden da kuma Trump idan an yi maganar dangantar Amurka da HKI.

Yace dukaninsu mashaya jinin Falasdinawa ne, kuma sune suke gudanar da harkokin shugabancin Amurka a bayan fage. Banda haka su ne wadanda suke da biliyoyin dalar Amurka wadanda suke jujjuya duniya da su.  

Yace: Amurka ta kara tallafin da take bawa HKI daga dalar biliyon 03 zuwa dalar biliyon 24 a wannan shekara wanda ya nuna cewa zasu ci gaba da yaki da kuma zubar da jin Larabawa ne fiye da kisan kiyashin da suka yi watani 15 da suka gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments