Wani Harin Isra’ila Ya Yi Ajalin Falasdinawa 27 A Khan Younis

Majiyoyin lafiya a Falasdinu na cewa adadin mutanen da suka rasa rayukansu a wani hari da Isra’ila ta kaddamar a yankin Khan Younis ya kai

Majiyoyin lafiya a Falasdinu na cewa adadin mutanen da suka rasa rayukansu a wani hari da Isra’ila ta kaddamar a yankin Khan Younis ya kai  akalla 27.

Tunda farko da bayanai sun nun cewa kan harin da Isra’ila ta kai a gabashin Khan Younis da ke kudancin Gaza wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 17.

Majiyoyin lafiya sun shaidawa tashar Al Jazeera ta Larabci cewa adadin wadanda suka mutu ya kai 27.

A halin da ake ciki kuma, a Deir el-Balah da ke tsakiyar Gaza, wani harin bam da Isra’ila ta kai kan wani gida ya kashe Falasdinawa akalla biyu tare da jikkata wasu da dama, a cewar kamfanin dillancin labarai na Wafa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments