Wani Dan Majalisar Dokokin Kasar Amurka Ya Bukaci Amurka Ta Jefa Makaman Nukliya Kan Gaza

Wani dan majalisar dokokin kasar Amurka daga jam’iyyar Republican daga jihar Florida Randi Fine ya bukaci gwamnatin Amurka ta yi amfani da dimbin makaman N

Wani dan majalisar dokokin kasar Amurka daga jam’iyyar Republican daga jihar Florida Randi Fine ya bukaci gwamnatin Amurka ta yi amfani da dimbin makaman N uklkiya da ta tara don kawo karshen yaki a gaza, ta kashe dukkan Falasdinawa a lokaci guda a huta.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Fine yana fadar haka a wata hira da ta hadashi da tashar talabijin ta Foxnews a jiya Alhamis.

Ya kuma  kara da cewa Amurka bata shiga tattaunawa da sojojin Nazi a yakin dunbiya na biyu ba, bata kuma yi kome bas ai da ta yi amfani da makaman nuklioya a kan Hiroshima da kuma Nagasafi sai kasar Japan ta mika kai ba tare da wasu matsala ba.

Fine yace a yanzun ma al-amarin ya kai ga zabin amfani da Nukliya kan Gaza kawai ta rage.

Labarin ya kara da cewa wannan bas hi ne karon farko wanda Randy Fine yake kiran gwamnatin Amurka ta yi haka ba. Kuma ya sha suka daga kungiyoyi daban daban.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted