Rundunar ruwa ta dakrun kare juyin musulunci ta Iran ta sanar da cewa wani jirgin ruwa dakon man man fetur da ya bi ta barauniyar hanya a mshigar Ruwan Hurmuz ya taka nakiya da hakan ya yi sanadiyyar fashewarsa.
Sanarwar ta ci gaba da cewa; jirgin Ruwan yana dauke da man fetur da ya kai ganga miliyan biyu da ya taka nakiyar da ta yi sanadiyyar tashin gobara a cikinsa.
Bugu da kari wannan jirgin Ruwan ya kashe na’urar da take nuna inda yake tafiya saboda kar a gane shi, kuma ya so wucewa ne ta mashigar Ruwan Hurmuz ta hanyar ingiza mai kantu Ruwan da sojojin ‘yan ta’adda na Amurka suka yi masa.
Dakarun kare juyin musuluncin na Iran sun kuma jaddada cewa; mashigar Hurmuz a kulle take, don haka duk wani jirgin Ruwan da zai yi tunanin bi ta barauniyar hanya, to zai kone saboda dogaro da sojojijn ‘yan ta’addar Amurka da ya yi.