Wakilin Hukumar FAO A Iran Yace Sauyin Yanayi Ya shafi Dukkan Yankin

Wakilin hukumar abinci na noma ta duniya FAO, Farrukh Toirov, ya bayyana cewa sauyin yanayi ya shafi dukkan kasashen yankin Asiya da kudu, don haka

Wakilin hukumar abinci na noma ta duniya FAO,  Farrukh Toirov, ya bayyana cewa sauyin yanayi ya shafi dukkan kasashen yankin Asiya da kudu, don haka yana daga cikin ayyukansu su samar da sabbin dabarbanun ayyukan noma tare da kasar Iran. Sannan JMI a matsayin kasa wacce take tsakiyar kasashen yankin tana iya aika da wadan nan dabarbaru ga sauran kasashen yankin.

Kamfanin dillancin labaran Iran Press ko IP na kasar Iran ya nakalto Farrukh Toirov yana fadar haka, a dai-dai lokacinda ya mika takardun kama aiki a nan Tehran, daga babban cibiyarsu a MDD.

Sabon wakili FAO a Iran ya kammala da cewa hukumarsa zata yi aiki tare da makarantu da cibiyoyin ayyukan noma don aiki tare da kuma samun nasarar kaiwa ga natija mai kyau wajen shawo kan sauyin yanai a kasar da kuma yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted