Wakilan Hamas sun isa Alkahira don shawarwarin tsagaita wuta a Gaza

Wata majiyar Falasdinawa ta shaida wa AFP cewa “Masu shiga tsakani na aiki don samar da wata hanyar cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta” wadda za

Wata majiyar Falasdinawa ta shaida wa AFP cewa “Masu shiga tsakani na aiki don samar da wata hanyar cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta” wadda za ta sa a sako dukkan sauran fursunonin da ake tsare da su a Gaza “a rukuni guda.”

Shawarar na iya hadawa da “tsagaita bude wuta na kwanaki 60, sannan kuma a yi shawarwarin tsagaita bude wuta na dogon lokaci, da kuma yarjejeniyar musayar dukkan fursunonin Isra’ila da suke da rai da wadanda suka mutu, a cikin rukuni guda,” a cewar majiyar.

Tawagar kungiyar Hamas karkashin jagorancin Khalil al-Hayya ta isa kasar Masar domin halartar shawarwarin tsagaita wuta a zirin Gaza.

Tun da farko dai kamfanin dillancin labaran AFP ya nakalto wasu majiyoyi suna cewa wasu manyan mambobin Hamas na kan hanyar zuwa Alkahira domin ganawa da jami’an Masar a wani bangare na kokarin shiga tsakani. Wata majiya ta lura cewa ziyarar ta kasance “bisa gayyatar Masar,” ta kara da cewa al-Hayya zai gana da jami’ai “don tattauna sabbin abubuwan da suka faru a tattaunawar tsagaita bude wuta da musayar fursunoni.”

Wani kusa a Hamas ya shaidawa AFP cewa kungiyar “ba ta sami wata sabuwar shawara daga bangaren Isra’ila ta hanyar masu shiga tsakani ba, amma tana nan a shirye don cimma yarjejeniyar idan Isra’ila ta yanke shawara.”

Ya jaddada cewa Hamas na neman kawo karshen yakin na dindindin, da kuma dage takunkumin da Isra’ila ta kakaba na hana shigar da abinci da kayan agaji zuwa yankin Zirin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments