To anan Malam ya yi kokarin yi mana baya da cewa akwai ra’ayoyi guda Uku kan batun yin azaba cewa shin ya alaƙar azabar nan da aikin da Mutum ya ki aikatawa ko ya aikata.? 1-Wasu na kallon babu wata alaƙa tsakaninsu. 2- Wasu kuma na ganin akwai alakar amma azabar ba da wuri take zuwa ba sai bayan mutuwa ba kai tsaye lokacin da ka aikata sabon ba ko kabar wajibin. 3- Wasu na kallon alaƙar cewa a ‘a kai tsaye mutum yake samun saka makon aikin da ya yi ko ya ki aikatawa illa dai ita wannan duniyar ba wuri ne da mutum zai iya jin wannan azabar ba sai ranar da Allah ya yaye wannan kashafin ya dau ransa zai fahimci ashe kai tsaye lokacin da kayi aikin da ka cancanci azaba azabar take tare da kai.