Na Farko Malama tayi bakin iyawarta da duk abin da ta sani na bayyanawa masu kallo mene ne ake cewa hawan jini a mahangar Lafiya da Yanda ilimin ke kwallon hadarin hawan jinin da.
Na biyu Malamar ta yi kakari sosai Wurin bayyanawa masu kallo cewa akwai wasu hanyoyi da Mutum zai iya binsu domin sassauta hawan jinin ga Mutum da ya riga ya kamu da kuma kare kai ga wanda bai riga ya kamun ba.
Sannan ta bayyana Alamomin hawan jinin ta yanda duk wani mai kwallon da ya lura yana da waɗannan alamomin a jikin sa ya sanya ya kamata ya nufi asibiti domin kwararrun likitocin lafiya dake da masaniya kan cutar ta hawan jini su dora shi a kan Hanyar magancewa ko kuma sassauta hadarin cutar.
Sannan Malama ta tabo Abinda Ya shafi Ciwon Gabobi wanda shima nau’i ne na ciwon da ake fama dashi a wannan Zamanin, wanda wasu daga cikin Mutane kan samu kansu a wannan cutar kuma suyi ta shan wahalar sakamakon basu tarbi cutar da wuri ba.