A cikin wannan tattaunawa Dr. Zahra Ridwan ta yi bayani a takaice a kan Cutar Malaria wadda take a matsayin cutar da tafi addabar al’ummomi da dama a nahiyar Afirka, wadda ke da alaka kai tsaye da cizon sauro, wanda shi kuma akwai abubuwa da suke zama musabbabin yaduwarsa a cikin muhalli, da kuma hanyoyin da ya kamata a bi wajen kare kai daga kamuwa ko kuma abin za a yi bayan kamuwa.