A cikin wannan shiri mun yi tattaki mun binciko wasu daga cikin shahararrun tsirrai na magani da ake amfani da su a Iran tun zamanin da. Shirin ya yi dubi kan sirrin da ke tattare da wasu tsirrai da suka hada da zafaran, isfand, sai kuma Ruwan wardi da ruwan na’a-na’a da sauran ganyaye da tsirran gargajiya, tare da nuna yadda ake amfani da su a al’adar Iran da kuma muhimmancinsu a rayuwar yau da kullum. Wannan shiri zai kai ku cikin duniyar magungunan gargajiya da sirrin dadaddun tsirrai da amfanin su a al’adun Iran.