Venezuela : An Tsare Wasu ‘Yan Amurka 3 Da Wasu ‘Yan Spain 2 Kan Zargin Hallaka Shugaba Maduro

A Venezuela ana tsare da wasu ‘yan Amurka uku da wasu ‘yan Spain biyu kan zargin yunkurin tayar da “hargitsi” a kasar. Ministan cikin gidan

A Venezuela ana tsare da wasu ‘yan Amurka uku da wasu ‘yan Spain biyu kan zargin yunkurin tayar da “hargitsi” a kasar.

Ministan cikin gidan kasar Diosdado Cabello ya fada a wani taron manema labarai a jiya Asabar cewa, an tsare mutanen biyar ne bisa zargin shirya kai hari kan shugaba Nicolas Maduro da gwamnatinsa.

Mista Cabelo ya ce hukumar leken asiri ta Amurka CIA ta jagoranci farmakin da aka kai da nufin hallaka Maduro.

Ministan ya shaidawa manema labarai cewa daya daga cikin Amurkawan da aka tsare an bayyana sunansa da William Joseph Castaneda Gomez, na US Navy.

Cabelo ya ce Gomez ne ke kula da kayyakin na CIA. Cabello ya kuma bayyana wasu Amurkawan biyu da ake tsare da su David Estrella da Aaron Barrett Logan.

Ministan ya ce baya ga Amurkawa 3, an kama wasu ‘yan kasar Spain biyu masu suna Jose Maria Basoa Valdovinos da Andres Martinez Adasme, baya ga wani dan kasar Czech Jan Darmovzal da ke da alaka da wannan makirci.

Ya ce hukumomi sun kwace bindigogi 400 kirar Amurka ga mutanen.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments