Babban jami’in diplomasiya a fadar Vatican ya bayyana cewa sama da shekaru biyu ke nan hki tana kai hare hare kan falasdinawa fararen hula a yankin Gaza adaidai lokacin da kasashen duniya suka kasa tsayar da kisan kare dangi da take yi a yankin da ta killace
Cardinal pietro parolin sakataren harkokin wajen fadar Vatican,shi ne yayi wannan bayani a taro na biyu da aka yi kan ambaliyar Aqsa mummunan harin da kuniyar Hamas ta kai wa Isra’ila a ranar 7 ga watan oktobn shekara ta 2023,
Tun daga lokacin gwamnatin yahudawan sahyuniya ta kaddamar da harin kan fararen hula a yankin Gaza inda ta yi sanadiyar mutuwar dubban falasdinawa da suka hada da mata da yara kanana, tare da lallata dukkan ababen more rayuwa , ta mayar da yankin tamkar kufaye,
Daga karshe babban jami’in na Vatican yayi kira da a dauki matakin mai tsauri kan gwamnatin yahudawan sahayuniya game da laifukan yaki da take tafkawa a gaza da kuma kawo karshen kisan kiyashin,