Uganda ta tura dakaru na musamman zuwa babban birnin Sudan ta Kudu

Rundunar sojan Uganda ta sanar da tura dakaru na musamman domin tabbatar da tsaro a babban birnin Sudan ta Kudu bisa bukatar Juba, a daidai

Rundunar sojan Uganda ta sanar da tura dakaru na musamman domin tabbatar da tsaro a babban birnin Sudan ta Kudu bisa bukatar Juba, a daidai lokacin da ake fargabar sake barkewar yakin basasa, musamman a halin da ake ciki tsakanin shugaban Sudan ta Kudu da mataimakinsa na farko.

A wannan Talata rundunar sojin Uganda ta sanar da tura dakaru na musamman zuwa Juba, babban birnin Sudan ta Kudu.

Kakakin rundunar sojin Uganda Felix Kulayigye ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, batun tura sojojin na zuwa ne bisa bukatar gwamnatin Sudan ta Kudu.

An kara samun tashin hankali a ‘yan kwanakin nan a kasar Sudan ta Kudu mai arzikin man fetur, bayan da gwamnatin shugaba Salva Kiir ta kame wasu ministoci biyu da wasu manyan jami’an soji da ke kawance da mataimakin shugaban kasar na farko Riek Machar. Tuni dai aka saki minista guda.

Kamen da aka yi a Juba da kuma kazamin fadan da ya barke a kusa da garin Nasir na arewacin kasar ana ganin zai kawo cikas ga yarjejeniyar zaman lafiya ta shekarar 2018 da ta kawo karshen yakin basasa na tsawon shekaru biyar tsakanin dakarun da ke biyayya ga Kiir da Machar inda aka kashe kusan mutane 400,000.

Bayan barkewar yakin basasa a Sudan ta Kudu a shekara ta 2013, Uganda ta aike da dakarunta zuwa Juba domin tallafawa dakarun Kiir da ke yaki da Machar. Daga karshe dai sojojin Uganda sun janye a shekarar 2015. An sake tura sojojin Uganda zuwa Juba a shekara ta 2016 bayan da aka sake gwabza fada tsakanin bangarorin biyu, amma kuma aka janye su daga bisani.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments