UAE Ta Bayyan Damuwarta Da Yadda Saudia Take Sanya Sunanta A Rikicin Kudancin Yemen

Gwamnatin hadaddiyar daular Larabawa UAE ta bayyana goyon bayanta ga tsaron kasar Saudiya sannan bata son a sanya sunanta a rikicin da ke faruwa tsakanin

Gwamnatin hadaddiyar daular Larabawa UAE ta bayyana goyon bayanta ga tsaron kasar Saudiya sannan bata son a sanya sunanta a rikicin da ke faruwa tsakanin bangarorin kudancin Yemen.

Tashar talabijan ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa, ma’aikatar harkokin wajen kasar UAE ta fitar da wani bayani wanda ya bayyana haka, kuma Almayadden ta samu kofin sanarwan ta gwamnatin UAE.

UAE ta musanta zargin ingiza wani bangare a kudancin Yemen don kai hari kan kasar Saudia, kuma bata son a sanya sunanta a cikin rikicn da ke faruwa a kudancin Yemen.

Bayanin ya kara da cewa, dangane da hare-haren da aka kaiwa jirgin ruwanta a tashar jiragen ruwa na Maklaa kuma, ta ce jirgin baya dauke da makamai, kuma ababen hawan da aka saukar na sojojinta da suke aiki a kudancin Yemen ne. ba na wani daga cikin bangarorin da suke rigima a yankin ne ba.

Banda haka bata kai wadan nan kayaki zuwa kudancin Yemen ba sai tare da amincewar kasar Saudiya karkashin hadakan kasashen larabawa. Don haka ta yi mamakin yadda aka maiwa jirgin nata hari.  Kafin haka dai shugaban majalisar jagorancin kudancin Yemen Rashaad Al-Alimi ya buka ce UAE ta fidda sojojinta daga kudancin Yemen a cikin sa’o’ii 24 masu zuwa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted