Kafafen yada labaran gwamnatin yahudawan Isra sun yi tsokaci kan Jawabin babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon dangane da ayyukan kungiyar na fuskantar barazanar Isra’ila.
A rahoton al-Mayadeen, bayan kammala jawabin na Sayyid Hasan Nasrallah, babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon, kafofin yada labaran gwamnatin sahyoniyar sun mayar da martani a kai tare da bayyana jawabin nasa a matsayin mafi karfi tun bayan fara yaki a cikin watanni fiye da takwas.
Wadannan kafafen yada labarai sun jaddada cewa: Nasrullah ya kuduri aniyar ci gaba da yakin da ake yi a halin yanzu don kare Gaza har sai an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, kuma bai amince da barazanar Tel Aviv da masu shiga tsakani ba.
Har ila yau, kafofin yada labaran gwamnatin Sahayoniya sun yarda cewa: Sojojin Isra’ila ba a shirye suke da kowane irin yanayi a Gaza ko Lebanon ba.
Tashar talabijin ta Zionist Kan TV ta mai da hankali kan barazanar da babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya yi wa kasar Cyprus kan taimakon Isra’ila wajen kai hari a Lebanon da Gaza, ta ce wannan batu na nuni da kololuwar fahimta da kuma irin masaniyar da Sayyid Hasan Nasrallah yake da ita kan halin da ake ciki da kuma abin da ke kai yana komowa a bayan fage.