Wata tsohuwar ministan kasar Spain ta kwatanta kisan kiyashin da ake yi a Gaza da gidajen gas na Nazi a Jamus
Shugabar jam’iyyar Podemos ta masu sassaucin ra’ayi a kasar Spain Ione Belarra ta kwatanta mutuwar Falasdinawa da suka rasa matsugunansu da suke rayuwar tantuna a asibitin shahidan Al-Aqsa bayan wani harin bama-bamai da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai kan su, da kisan kiyashin da ake riya cewa an yi wa yahudawa a kasar Jamus a gidajen gas na Nazi.
Belarra ta ce, tana mamaki: Mene ne bambanci tsakanin wannan hari da yahudawan sahayoniyya suke ƙona Falasdinawa a Gaza da ɗakunan gas na Nazi?
A baya Belarra ta soki fira ministan kasar Spain Pedro Sanchez da kungiyar Tarayyar Turai saboda rashin nuna cikakken martani kan ‘yan sahayoniyya da suke cin karensu ba babbaka a kan Falasdinawa.
Ta yi nuni da cewa: Brussels ita ce wurin da dole ne ta daukin matakan matsin lamba kan fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu domin cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta hakika, kuma ita ce wurin da za a sanya takunkumin tattalin arziki da takunkumin hana sayar da makamai ga yahudawan sahayoniyya da magoya bayansu.