Tsohonn Shugaban Kasar Siriya Ya Bayyana Dalilan Barinsa Kasarsa A Farkon Wannan Watan

Kafafen yada labaran kasar Rasha da kuma na wasu kasashen larabawa sun watsa labaria dangane da yadda tsohon shugaban kasar Siriya Bashar Al-Asad ya fice

Kafafen yada labaran kasar Rasha da kuma na wasu kasashen larabawa sun watsa labaria dangane da yadda tsohon shugaban kasar Siriya Bashar Al-Asad ya fice daga kasar.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto daga shafin Telegrame na tsohon shugaban kasar ta Siriya, ya na bayanin yadda shugaban ya kasance a ranar da yan ta’adda da kuma masu adawa da gwamnatinsa suka kwace kasar birnin Damascus babban birnin Kasar.

Asad ya bayyana cewa har zuwa karfe 8 na safe a ranar Lahadi 8 ga watan Decemba na shekara ta 2024 ya na birnin Damascus babban birnin kasar ta Siriya, yana kuma bibiyar abubuwan da suke faruwa da kansa. Yace batun ficewa daga kasar da kuma neman mafaka a wata kasa bai zo masa ba.

Tsohon shugaban ya ce: a lokacinda yan ta’adda da masu adawa da gwamnatinsa suka shiga birnin Damascus, kuma har aka bayyana wani a matsayin shugaban kasa ne, ya ga cewa babu bukatar ya ci gaba da zama cikin kasar.

Tsohon shugaban yace har yanzon tunaninsa shi ne sake kwace kasar Siriya daga matsalolin da ta fada ciki, bayan da yan’adawa da kuma yan ta’adda suka dare a kan madafun ikon kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments