Tsohon Jami’in Sojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Ya Ce: Batun Kawo Karshe Hamas Mafarki Ne

Tsohon babban jami’in kula da korafe-korafen sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila ya bayyana cewa: Haramtacciyar kasar Isra’ila tana kan hanyar rushewa nan kusa kadan Manjo Janar

Tsohon babban jami’in kula da korafe-korafen sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila ya bayyana cewa: Haramtacciyar kasar Isra’ila tana kan hanyar rushewa nan kusa kadan

Manjo Janar Yitzhak Brik tsohon jami’an sojin ko-ta kwana kuma tsohon mai kula da korafe-korafen sojoji a cikin rundunar mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi gargadin rugujewar Isra’ila a cikin shekara guda, idan yakin da take ci gaba ya kai ga matakin murkushe kungiyoyin gwagwarmayar Musulunci ta Hamas da Hizbullah.

A labarin da jaridar yahudawan sahayoniyya ta Haaretz ta buga, Brick ya ce: Ministan yakin haramtacciyar kasar Isra’ila Yoav Gallant ya fara fahimtar gaskiya, wato: Idan yaki ya barke a dukkan yankin Gabas ta tsakiya saboda rashin cimma matsaya kan Gaza, to lallai haramtacciyar kasar Isra’ila za ta kasance cikin babban hatsari.

Brick ya kara da cewa: Mafi yawan kalaman marasa tushe da Gallant ya yi dangane da manufofin yakin Zirin Gaza har yanzu ba a cimma nasara ba. Kuma bayan shigar sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila cikin yankin Gaza, Gallant ya ce: Za su mamaye birnin da rusa hanyoyin karkashin kasa, sannan zasu yi galaba a kan kungiyar Hamas, wanda hakan wani al’amari ne da ba zai yiwu ba.

Brik ya yi nuni da cewa, Gallant ya kuma yi ikirarin, a lokacin da ya kai hari a Khan Yunis da ke kudancin zirin Gaza, cewa Yahya Al-Sinwar na cikin ramuka shi kadai, kuma ya rasa iko da mutanensa, kuma wannan ba gaskiya ba ne.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments