Daya daga cikin manyan-manyan jami’an gwamnatin tsohon shugaban kasar Amurka Joe Biden, ya bayyana cewa: “Babu tantama gwamnatin HK Isra’ila ta tafka laifukan yaki a kan Falasdinawa a zirin Gaza da ta killace.
Matthew Miller wanda ya yi aiki a matsayin kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka tun daga 2023 har zuwa karshen gwamnatin Joe Biden, ya fada wa tashar talabijin ta Sky News kan cewa; Isra’ilan ta tafka laifukan yaki.
Da aka yi masa tambaya a kan yakin Gaza a fadar White House, Miller ya ce; An yi ta samun tsabani dangane da yakin, sabani manya-manya wani lokacin kuma kananan sabani, kan yadda za a kare dangantakar Amurka da HK Isra’ila duk tare da abinda take aikatawa.”. Amma Miller ya tabbatar da cewa HK Isra’ilan ta tafka laifukan yaki wanda babu shakka a cikin hakan..
Da aka tambaye shi a kan, ko me ya sa a lokacin suke Mulki bai bayyana cewa HK Isra’ila tana aikata laufkan yaki ba? Sai ya amsa da cewa:
“Idan mutum yana cikin gwamnati, ba ya bayyana ra’ayinsa na kashin kansa, yana bayyana ra’ayin gwamnatin Amurka ne.”
Haka nan kuma ya ce; Aikin mai magana da yawun gwamnati, ko dai ka zama mai Magana da yawun shugaban kasa, ko gwmanatin kasar, amma idan baka cikin gwamnati, to za ka iya fadar ra’ayinka.”