Tsohon jami’an MDD Yayi Tir Da Amincewa Da Kudurin Amurka A Kwamitin Sulhu Kan Gaza

Rahotanni sun bayyana cewa Craig mokhiber tsohon babban jami’in hukumar kare hakkin dan adam na majalisar dinkin duniya ya sanar a hukumance yin Allah wadai

Rahotanni sun bayyana cewa Craig mokhiber tsohon babban jami’in hukumar kare hakkin dan adam na majalisar dinkin duniya ya sanar a hukumance yin Allah wadai da kuri’ar amincewa da kudurin Amurka da aka yi a kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya na aikewa da dakarun kasashen waje zuwa yankin Gaza yace wannan baban abin kunya ne.

Kalaman nasa ya nuna irin suka da kungiyoyin kasa da kasa suke yi ne kan mummunan tasirin da yakin yayi wa yankin gaza, da kuma kasa tsagaita wuta da yadda za’a shigar da kayayyakin agaji zuwa yankin

Isra’ila ta toshe kafar shigar da magunguna da kayayyakin lafiya da kuma hana fitar da marasa lafiya sama da 16500 zuwa wajen don yi musu maganin, bayan da cibiyoyin kula da lafiya suka rushe baki daya ya bar marasa lafiya da dama a yashe ba tare da kulawa ba.

Daga ranar 7 ga watan oktoban shekara ta 2023 da isra’ila ta kaddamar da hari kan gaza  zuwa yanzu Kimanin mutane 68872 ne suka yi shahada akalla  170,000 kuma suka jikkata dubbai kuma sun bace bata sama ko kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments