Tsohon fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Naftali Bennett ya yi kira ga yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida da kada su bar haramtacciyar kasar Isra’ila da take cikin mawuyacin hali tun shekara ta 1948.
A rubutun da ya yi a dandalin X – a jiya Laraba, ya yi kira ga tsagerun yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida da kada su dauki matakin gudu daga haramtacciyar kasar Isra’ila ta hanyar yin hijira zuwa wasu kasashen duniya.
Bennett ya kara da cewa: Wata injiniya wanda bai ambaci sunanta ba ta shaida masa cewa: Za su yi kaura daga haramtacciyar kasar Isra’ila zuwa wasu kasashen Turai kafin fara shekarar karatu ta gaba a farkon watan Satumba mai zuwa), don haka ya shiga bakin ciki mai tsanani.
Ya jaddada cewa: Suna cikin yanayi mafi wahala tun bayan Yaƙin ’Yancin kai (Nakba na shekara ta 1948), kuma duniya ta ƙaurace musu ga kuma yahudawan sahayoniyya kimanin 120 a matsayin fursunonin yaki, baya ga dubban iyalai da suka rasa ‘yan uwansu, sannan mazauna yankin Galili da ke arewacin haramtacciyar kasar Isra’ila sun gudu, kuma dubbai sun yi hijira, sannan jami’an gwamnati ba su damu da kowa ba sai kawunansu kawai, ga tabarbarewar harkar tattalin arziki da raunanar rundunar tsaron haramtacciyar kasar ta Isra’ila.