Trump Ya Kakabawa Wata Jami’in MDD Takunkumi Bayan Ta Fallasa Laifukan HKI Da Hannun Amurka A Ciki

Gwamnatin kasar Amurka ta dorawa wata ma’aikaciyar MDD takunkumi saboda yadda take amfanin laifukan yaki da take yi a gaza da kuma irin tallafin da

Gwamnatin kasar Amurka ta dorawa wata ma’aikaciyar MDD takunkumi saboda yadda take amfanin laifukan yaki da take yi a gaza da kuma irin tallafin da Amurka take bawa HKI yasa tana da hannun a kissan kiyashin.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa sakataren harkokin wajen kasar Amurka Marco Rubio ya bayyana cewa shi ya sa hannu a kan umurnin takunkuman da aka dorawa Francesa Albanese, jami’a mai kula da tattara bayanai na musamman a kan Falasdinu ga hukumar kare hakkin bil’dama da MDD.

Rubio ya bayyana cewa sanadiyyar rahoton ta ne kotun ICC ta fidda samacin kama Banyamin Natanyaho, da kuma tsohon ministansa na Tsaro Yoav Galant. Banda haka takan bada rahoto kan yadda Amurka da wasu kasashen yamma suke aikawa HKI makamai.

Sannan ya ce: Albanese tana yawan amfani da Kalmar kissan kiyashi a rahotonta. A watan da ya gabata ta bukaci a sanyawa HKI takunkuman tattalin arziki mai tsanani. A wani lokacin kuma ta bukaci majalisar ta kori HKI daga MDD.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted