Steve Witkof wakilin gwamnatin Amurka na musamman a yammacin Asia ya bayyana cewa, shugaban kasar Amurka Donal Trump ya damu da yadda Iran ta yi ta mika kai ga bukatarsa ta cimma yarjeniya da Amurka kan shirinta na makamashin Nukliya.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Witkof yana fadawa Lara Trump matar dansa .Ya kuma kara da cewa, shugaban ya tambayeshi da safe kan cewa ya damu da yadda Iran ta ki ta mika kai ga bukatunsa, duk da cewa yana da zabi da dama, amma abin yana damunsa.
Ya ce shugaban yana mamakin yadda ya tura sojojinsa na sama da kasa da ruwa don takurawa kasar amma ba wata alama ta mika kai ga bukatunsa, basu zo suka ce basa bukatar makaman nukliya kuma ga abinda muke son yi.
Wirskof yana riya cewa wai Iran ta gasa makamashin Uranium fiye da yadda take bukata don aikin da ba na soje ba. Amurka dai tana son Iran ta daina tashe makamashin Uranium kwata-kwata . Jakadan Amurka na musamman a yammacin Asia ya bayyana cewa, tare da umurninTrump ya gana da Reza Pahlavi dan sarkin da aka kora daga kasar. Amma bai bayyana abinda suka tattauna a kansa ba. A wani bangare kuma gwamnatin kasar Iran ta bayyana cewa, zata maida martani idan Amurka ko HKI sun kuskura sun maida mata martani. Fiye da yadda suka maida martani a kan sansanin sojojin Amurka mafi girma a yanking abas ta tsakiya a yakin watan Yunin da ya gabata.