Trump : Isra’ila Na Taimakon Saudiyya A Yaki Da Yemen

Da aka tambaye shi akan batun yarjejeniyar Abraham da yiyuwar shigar Saudiyya a cikinta, Shugaban kasar ta Amurka ya ce, da akwai yiyuwar hakan ta

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya fadi cewa; Isra’ila tana taimakon Saudiyya, kuma Riyadh ta Aminta da hakan kuma tana jin dadi.

Shugaban kasar na Amurka ya kuma kara da cewa; Yana da kyakkyawar alaka da mahukuntan Saudiyya.

Donald Trump ya kuma kara da cewa; Tabbas Isra’ila ta bai wa Saudiyya taimako mai yawa.

Da kuma yake Magana akan yakin kasar Ukiraniya, shugaban kasar ta Amurka ya ce, yana son kawo karshen yakin, kuma a halin yanzu yana ttataunawa da shugabannin Ukiraniya da na Rasha.

Da aka tambaye shi akan batun yarjejeniyar Abraham da yiyuwar shigar Saudiyya a cikinta, Shugaban kasar ta Amurka ya ce, da akwai yiyuwar hakan ta faru.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted