Trump : Falasdinawa Ba Su Da Hakkin Komawa Gaza Bayan Kwace Yankin

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa shirin korar  al’ummar Zirin Gaza zai hada da kwace ‘yancinsu na komawa kasarsu. Trump ya fada a wata

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa shirin korar  al’ummar Zirin Gaza zai hada da kwace ‘yancinsu na komawa kasarsu.

Trump ya fada a wata hira da tashar Fox News cewa shirin da yake yi a kan Gaza ya kunshi fitar da daukacin al’ummar yankin da kuma sake gina abin da ya kira ‘’Sake farfado da Gabas Ta Tsakiya’’

Ya kara da cewa za a iya samun wurare daban-daban har guda shida don Falasdinawa su zauna a wajen zirin Gaza.

Ya kuma ce za’a gina wa Falasdinawa gidaje masu kyau da inganci nesa da wajen da suke, saidai bai bayyana takamaiman wuri ba.

A wani labarin kuma Donald Trump ya fada a ranar Litinin din nan cewa cewa “watakila” zai daina ba da taimako ga Masar da Jordan idan ba su karbi Falasdinawa daga Gaza ba.

Kasashen biyu dai duk sun yi fatali da shirin na Trump.

Ko a ranar Litinin din masar ta yi watsi da “duk wani sulhu” da ke tauye hakkin Falasdinawa mazauna Gaza, bayan da ministan harkokin wajen kasar ya gana da takwaransa na Amurka a birnin Washington.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments