Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya sanya hannu a dokar zaben da aka yi wa kwas-kwarima, kwana guda bayan da majalisun dokokin kasar suka amince da ita.
A jiya laraba ce shugaba Tinubu ya sanya hannu kan dokar, a wani taro da ya gudana a fadarsa da ke Abuja, wanda ya samu halartar shugaban majalisar dattawar kasar Godswill Akpabio da kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abbas.
An dai kwashe tsawon watanni ana tafka muhawara kan gyaran fuskar da aka yi wa dokar, lamarin da ya haifar da zazzafar muhawara a makon da ya gabata bayan wasu ƴan Najeriya da kuma ƴan majalisa na jam’iyyar adawa, suka nuna kin amincewa da bangaren dokar da ya yi bayani kan tura sakamakon zabe.
A ranar Talatar data gabata ne dai majalisar dattawar Najeriya tabi sahun ta wakilai wajen amince da dokar da ta bada damar yin amfani da na’ura ko kuma takardu idan aka samu tangardar internet wajen tura sakamakon zabe.
Masu ruwa da tsaki dai na ganin tura sakamakon zabe kai tsaye daga runfunan zabe ta hanyar Internet, zai taimaka a kokarin da ake yi na magance magudin zabe a kasar.