Kafafen yada labarai a kasar Masar sun bayyana cewa tattaunawar tsagaita wuta a Gaza, tsakanin HKI da kuma kungiyoyin Hamas da Kawayenta a Gaza, ya kama hanyar rushewa saboda wasu sharudda wadanda HKI ta kawo wadanda kuma kungiyar Hamas da sauran Falasdinwa ba zasu taba amincewa ba.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto wasu jami’an gwamnatin kasar Masar wadanda suke kai kawo tsakanin Alkahira da Doha don tabbatar da cewa an tsagaita wuta a Gaza, suna fadar haka. Sun kuma kara da cewa gwamantin HKI ta kawo wasu sharudda wadanda kungiyoyin falasdinawa wadanda suke fafatawa da ita ba zasu taba amincewa ba.
Mataimakin shugaban ‘kungiyar Jihadul Islami, Muhammad Al-Hindi ya bayyana cewa al-amura na tsagaita wuta suna tafiya kamar yadda aka tsara, wato a cikin marhaloli uku, amma sai kwatsam HKI ta kawo wasu sharudda wadanda ba zai yu falasdinawa su amince da su ba.
Sai dai ya ce, ba’a fidda tsammanin tsagaita wutar zata wanzu ba, don mai yuwa a tsallaka wannan matsalar a cikin kwanaki masu zuwa. Amma gaskiyar al-amarin tattaunawar tana tangal-tangal kuma baa bin mamaki idan ta rushe ba.