Tashar jiragen sama ta birnin Beirut tana cike da masu shiga kasar daga kasashen daban-daban don halattar jana’izar Shahidai kuma shuwagabannin kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasarallah da kuma Magajinsa Shahid Sayyid Hashimi Safiyyuddeen wanda za’a gudanar a ranar 23 ga watan Fabarairu da muke ciki.
Kamfanin tafiye-tafiye na “Ajuz Travillin Agency’ ya fadawa tashar talabijin ta Almanar kan cewa tun yawan jiragen sama masu zuwa daga kasashen waje suka nin nink tafiye-tafiyensu zuwa Beiru, daga cikinsu, akwai Iraq Air wanda yake zuwa Beiru har sau biyu. Amma daga yau ya kara shi zuwa har sau ukku.
Kamama Egypt Air ya ninka zuwasa Beirut har sai yu. Da kuma Tarksih Air shi ya ninninka ta fiyasa zuwa kasar.
Labarin ya kara da cewa daga ranakun 20-22 ga watan Fabrairu ne ake saran samun masu zuwa Beirt mafi yawan don samun halattar jana’izar manya-manyan shidan.
HKI ce ta yi ruwan boma bomai kan sayyid Hassan nasaralla wanda ya kai ton 85 wanda ya kai shi ga shahada a shekarar da ta gabata, sannan kwanaki bayan haka ta kashe magajinsa Sayyid Safiyuddeen. A yakin watin 15 da kungiyar Hizbullah ta faffata da HKI.