Taron Kasashen Turai Don Goyon Baya Ga Kasar Ukraine, Ya Watse Ba Tare Da Tsaida Irin Taimakon Da Zasu Yi Mata Ba

Shuwagabannin kasashen Turai da wakilai daga kasashe 19 na Kungiyar, sun kammala taro a birnin Lodon, inda suka nuna goyon bayansu ga kasar Ukraine, musamman

Shuwagabannin kasashen Turai da wakilai daga kasashe 19 na Kungiyar, sun kammala taro a birnin Lodon, inda suka nuna goyon bayansu ga kasar Ukraine, musamman kan yadda ya dage wajen kare kasarsa da kasashen Turai  a gaban Donal Trum a ranar Jumma’an da ta gabata, ya waste ba tare da kasashen sun bayyana abinda zasu iya yiwa Ita Ukraine a yakin da take ci gaba da fafatawa da Rasha ba.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa matsalolin da suka taso dangane da dogaron da kasashen turai suke yi kan kungiyar Tsaro ta NATO yana daga cikin manya-manyan al-amura da suka tattauna.

Yakin cacarbakin da shugaba Trump na Amurka yayi da shugaban kasar Ukraine ya zama masomin kawo sauye-sauye masu yawa a dangantakar kasashen da Amurka.

Firai ministan kasar Ukraine Keir Starmer ya gabatar da shawara mai matakai 4 ta taimakawa kasar ta Ukraine a yakin da taek fafatawa da kasar Rasha. Sannan shuwagabannin kasashen turai sun bukaci a samar da wata cibiyar tsaron kasashensu ba tare da dogaro da kasar Amurka ba.

Har’ila yau shugaban kungiyar tarayyar ta Turai Ursula Von der Leyen ya bukaci a gaggauta samar da hanyar tsaron kasashen na turai da gaggawa.

 

 

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments