Taro Kan Sabon Salon Mulkin Mallakar Faransa A Afrika

Azerbaijan an gudanar da wani taro kan ”manufofin Faransa na sabon salon mulkin mallaka a nahiyar Afirka”. Wata kungiya ce mai zaman kanta ta Baku

Azerbaijan an gudanar da wani taro kan ”manufofin Faransa na sabon salon mulkin mallaka a nahiyar Afirka”.

Wata kungiya ce mai zaman kanta ta Baku Initiative Group (BIG) ce ta shirya taron a Baku, babban birnin kasar Azabaijan.

Masu jawabi a taron sun dinga sukar Faransa da kakkausar murya a kan yadda take ci gaba da tsoma baki cikin al’amuran kasashen da ta yi wa mulkin mallaka a baya.

Taron na ranar Alhamis ya zo ne a daidai lokacin da kasashen Afirka da dama ke ci gaba da samun karuwar kiraye-kirayen neman ‘yancin kai, musamman ma dangane da dangantakarsu da Faransa da wasu Ƙasashen Yammacin Duniya.

Kasashen Nijar da Burkina Faso da Mali duk sun kawo karshen huldar soji da kasar ta faransa, a shekarun baya-bayan nan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments