Tankokin Yakin Isra’ila Sun Kutsa Cikin Tsakiyar Birnin Rafah

Rahotanni daga Gaza na cewa sojojin mamaya na Isra’ila sun kutsa cikin birnin Rafah da tankokin yaki, lamarin daya kara sanya firgici a jama’ar dake

Rahotanni daga Gaza na cewa sojojin mamaya na Isra’ila sun kutsa cikin birnin Rafah da tankokin yaki, lamarin daya kara sanya firgici a jama’ar dake yankin kwana biyu bayan kazamin harin da ya yi sanadin mutuwar gomman mutane a sansanin ‘yan gudun hijira na Rafah.

Matakin na zuwa a daidai lokacin Majalisar Dinkin Duniya ke shirin tsara wani daftarin kudiri na kokarin “dakatar da” tashin hankalin a wurin bayan harin sojojin Isra’ila da ya  hadassa fushin duniya.

Bayanaui sun ce bayan kusan makonni uku da kai hare-hare ba kakkautawa kan Rafah, yanzu tankunan yankin na Isra’ila sun kutsa cikin birnin dake kudancin Gaza.

A wani labarin kuma kungiyoyin farar hula a Gaza, sun sanar a wannan Talata, cewa, Isra’ila ta kai wani sabon kazamin hari a sansanin ‘yan gudun hijira da ke yammacin Rafah, kasa da kwanaki biyu bayan wani harin makamancin haka wanda ya yi sanadin mutum 45 ciki har da yara da mata.

Muhammad Al-Mughair, wani jami’in tsaron farar hula na Falasdinu, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa mutane 21 ne suka mutu a wannan harin da aka sake kaiwa kan tantunan ‘yan gudun hijira a yammacin Rafah.

Share

4 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments