Rahotannin da suke fitowa daga yankin Gaza sun ce, tankokin ‘yan mamaya sun killace daruruwan mata da kananan yara a Arewacin Gaza domin tilasta su ficewa daga cikinsa.
Jami’in ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza Munir Ibrahim ya bayyana cewa; Yadda ‘yan mamayar suke tara mata da kananan yara suna tilasta musu fircewa daga Areewacin zirin gaza, zuwa birnin Gaza, ba komai ba ne sai kisan kare dangi, kuma yana cin karo da dokokin kasa da kasa.
Kwanaki 20 kenan a jere, sojojin mamayar suna kai hare-hare ta sama akan Beit Lahiya da Jabaliya da salon da ya yi daidai da kisan kare dangi.
A cikin kwanaki kadan da su ka gabata, sojojin mamata sun kunna gobara a cikin wasu hemomi na ‘yan gudun hijira a Arewacin Gaza, haka nan kuma budewa farafen hula wuta da yi musu kisan gilla. Bugu da kari ‘yan mamayar sun hana shigar da kayan abinci a cikin yankin da hakan ya jefa mutane cikin yunwa da tamowa ta kananan yara.
Sojojin na mamaya suna kai wadannan munanan hare-haren ne dai akan fararen hula ‘yan gudun hijira a karkashin cikakken goyon baya da kuma taimakon Amurka.
Daga shekarar da ta gabata zuwa yanzu adadin wadanda su ka yi shahada da jikkata a Gaza sun kai 143,000, sai kuma wasu fiye da 10,000 da su ka bace.