Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa a cikin sa’o’i kadan da su ka gabata, jiragen yakin HKI sun kai hare-hare da bama-bamai 1800 akan cibiyoyi 50 a cikin kasar Syria.
Majiyar ‘yan sahayoniyar ta kuma ce; An kai hare-haren de domin fasa da lalata dukkanin makaman tsaron sararin samaniya da Syriyan take da su.
Bugu da kari wannan majiyar ta kuma ce, abinda hakan yake nufi, shi ne Isra’ila za ta iya kai da komowa a sararin samaniyar Syria ba tare da wata damuwa ba.
A ranar Talatar da ta gabata sojojin Isra’ila sun ce, sun rusa kaso 70 zuwa 80% na makaman kasar Syria, a cikin sa’o’i kadan.
Daga cikin makaman da HKI ta rusawa Syria da akwai muhimman makamai masu linzami da ake harba su daga doron ruwa masu cin kilo mita 90 da kuma 190.
Har ila yau, sun kuma rusa wasu makamai masu linzamin da ake harba su daga kasa zuwa sama, da kuma daga kasa zuwa kasa. Sai kuma jirage marasa matuki, da wasu jiragen na yaki sai jirage masu saukar angulu na kai farmaki. Bugu da kari, Isra’ilan ta lalata tankokin yakin Syria, da na’urorin da ake harba makamai masu linzami daga kansu.