Ana ci gaba da yin kiraye-kiraye ga HKI da ta kawo karshen hare-haren da take kai wa kasar Syria,jim kadan bayan da sojojin HKI su ka sanar da cewa; a karon farko jirgin sama maras matuki na ‘yan sahayoniya ya sauka a Suwaidah.
A daren jiya Juma’a ne dai HKI ta kwana tana luguden wuta akan yankuna mabanbanta na kasar ta Syria da su ka hada da birnin Damascuss har da daurada fadar shugaban kasa.
HKI tana kai wannan hare-haren ne dai da sunan bayar da kariya ga ‘yan Duruz domin hana sojojin Syria ci gaba da kai musu hare-hare.
Jami’in diplomasiyyar MDD mai kula da kasar Syria Geir Otto Pedersen ya rubuta a shafinsa na X sakon yin tir da keta hurumin kasar Syria da Isra’ila take yi da su ka hada da birnin Damascus.
Haka nan kuma jami’in na MDD ya yi kira da a kawo karshen wadannan hare-haren akan Syria, da kauce kai wa farafen hula hari. Bugu da kari ya bayyana kai harin da cewa keta dokokin MDD ne da kuma kokarin hana tarwatsewar hadin kasar da ‘yancinta.
HKI ta bude kai hari ne akan kasar Syria da sunan kare ‘yan Duruz, da hakan yake kama hanya ce ta tarwatsa Syria da mayar da ita kananan kasashe.
Dama dai tun farko-farkon faduwar gwamnatin Syria, HKI take aiki tukuru domin ganin kasar ba ta ci gaba da zama a dunkule ba, ta tarwatse ra koma kananan kasashe.