Sudan Zata Canja Takardun Kudaden Kasar Saboda Magance Matsalar Sace-Sacen Kudade A Kasar

Babban bankin Sudan ya sanar da buga sabbin nau’o’in kuɗade domin maye gurbinsu da tsoffin kudaden kasar Babban bankin kasar ta Sudan ya bayyana cewa:

Babban bankin Sudan ya sanar da buga sabbin nau’o’in kuɗade domin maye gurbinsu da tsoffin kudaden kasar

Babban bankin kasar ta Sudan ya bayyana cewa: Kaddamar da sabbin nau’o’in kudin Sudan ya zo ne a matsayin madadin tsoffin kdaden kasar da ake amfani da su a halin yanzu, wanda amfani da tsoffin kudin zai kawo karshen yaduwa a hukumance a ranar 23 ga wannan wat ana Disamba, kuma mahukuntan kasar sun dauki wannan mataki ne a kokarin maido da darajar kudin kasar sakamakon wawashe dimbin kudaden kasar a lokacin yakin da ake yi a kasar tun tsakiyar watan Afrilun bara.

Tsarin musayar kudin wanda da farko ya fara ne da saka tsofaffin takardun kudi a asusun al’ummar kasar, kuma tsarin yana tafiya cikin kwanciyar hankali a kwanakin farko, amma an takaita fitar da kudin zuwa kudin kasar rufin da bai wuce fam dubu dari biyu ba, a wani shiri na neman al’ummar kasar su yi amfani da su a harkokinsu na yau da kullum.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments