Sudan Ta Fitar Da Kasafin Kudin Kasar Na Shekara Ta 2025 Duk Da Kalubalen Da kasar Ke Fuskanta

Majalisar Gudanar da mulkin Sudan da Majalisar ministocin kasar sun amince da kasafin kudin Sudan na shekara ta 2025 Zaman taron hadin gwiwa tsakanin majalisar

Majalisar Gudanar da mulkin Sudan da Majalisar ministocin kasar sun amince da kasafin kudin Sudan na shekara ta 2025

Zaman taron hadin gwiwa tsakanin majalisar gudanar da mulkin Sudan da na ministocin kasar ya amince da kasafin kudin shekara ta 2025, wanda ya hada da mayar da kashi 100 na albashin ma’aikatan kasar duk kuwa da manyan kalubalen da Sudan ke fuskanta.

Shugaban majalisar gudanar da mulkin Sudan, kuma babban hafsan-hafsoshin sojojin kasar Laftanar Janar Abdel Fattah Al-Burhan, wanda ya jagoranci taron a jiya Laraba, ya bayyana jin dadinsa ga kokarin da gwamnatin kasar ta yi dangane da kalubalen da kasar ke fuskanta, da kuma kishinta na samar da dukkan abubuwan da suka dace ga ‘yan ƙasa.

Al-Burhan ya yaba da rawar da bankin Sudan ya taka wajen sauya kudin da kuma shawo kan kalubalen da ke tattare da wannan tsari, yana mai jaddada muhimmancin gudanar da taruka domin shirya tsarurrukan sake gina kasar da ‘yan ta’addar suka lalata da suka hada da cibiyoyin gwamnatin Sudan da ke nufin rundunar Rapid Support Forces Ta Dakarun kai daukin gaggawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments