Sudan: An Bude Zirga-zirgar Jirage A Filin Saukar Jiragen Sama Na Khartum

Jirgin sama na farko da ya taso daga Port Sudan, ya sauka filin saukar jiragen sama na Khartum, babban birnin kasar Sudan. Wannan dai shi

Jirgin sama na farko da ya taso daga Port Sudan, ya sauka filin saukar jiragen sama na Khartum, babban birnin kasar Sudan.

Wannan dai shi ne karon farko da jirgin sama na kamfanin “Sudan Air”  ya sauka a filin saukar jiragen saman Khartum, tun bayan barkewar yakin basasar kasar a watan Aprilu na 2023.

Dama tun a ranar 26 ga watan Janairu ne dai gwamnatin Sudan a karkashin  Fira Ministan kasar Kamil Idris, ta yi taron farko a cikin birnin Khartum bayan da ta baro Port Sudan wanda ya zama matsugunin gwamnati na tsawon watanni 30.

Yaki a tsakanin sojojin kasar ta Sudan da kuma rundunar kai daukin gaggawa (RSF) ya barke tun a ranar 15 ga watan Aprilu na 2023, wanda ya zuwa yanzu ya ci dubban rayuka da kuma jikkata wasu dubun dubata. Haka nan kuma fiye da mutane miliyan 2 ne su ka zama ‘yan hijira acikin gida da kuma a kasashen makwabta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted