Sojojin Yemen Zasu Bullo Da Shirin Takurawa Jiragen Saman Haramtacciyar Kasar Isra’ila  

Dakarun gwagwarmayar kasar Yemen sun bayyana cewa: Za su mayar da jiragen saman yakin gwamnatin mamayar Isra’ila abin ba’a Shugaban majalisar koli ta siyasar kasar

Dakarun gwagwarmayar kasar Yemen sun bayyana cewa: Za su mayar da jiragen saman yakin gwamnatin mamayar Isra’ila abin ba’a

Shugaban majalisar koli ta siyasar kasar Yemen Mahdi al-Mashat, ya tabbatar da cewa: Tsaron sararin samaniyar sojojin kasar Yemen zai iya tunkarar jiragen saman yakin gwamnatin mamayar Isra’ila da suke kai hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yemen.

Shugaban majalisar koli ta siyasar kasar Yemen Mahdi al-Mashat ya shaidawa tashar talabijin ta Al-Mayadeen cewa: Kariyar tsaron sararin samaniyar sojojin Yemen za ta mayar da jirgin saman makiya ‘yan sahayoniyya abin izgili a cikin kwanaki masu zuwa.

Al-Mashat ya jaddada cewa: Sojojin kasar Yemen za su iya tunkarar jiragen saman yakin yahudawan sahayoniyya ba tare da haifar da wata illa ga zirga-zirgar jiragen sama da na ruwa ba,” yana mai cewa “labarin farin ciki da ke matsayin albishir” zai zo da zai zama ana murkushe jiragen saman makiya yahudawan sahayoniyya da suke amfani da shi wajen kai farmaki kan kasar Yemen.

Shugaban majalisar koli ta siyasar kasar Yemen ya yi ishara da cewa: An bayyana hanyoyin da makiya yahudawan sahayoniyya suke kaiwa kasar Yemen a matsayin wurare masu hadari ga dukkanin kamfanoni, domin tabbatar da tsaron zirga-zirgar jiragen sama da na ruwa a yankunan da sojojin kasar ke gudanar da ayyukansu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments