Search
Close this search box.

Sojojin Yemeni Sun Yi Amfani Da  Makaman Masu Linzami Kan Wani Jirgin Ruwan Da Ke Da Alaka Da HKI

Sojojin kasar Yemen sun bada sanarwan cilla wani sabon makami mai linzami don tarwatsa wani jirgin ruwa wanda yake da alaka da HKI a cikin

Sojojin kasar Yemen sun bada sanarwan cilla wani sabon makami mai linzami don tarwatsa wani jirgin ruwa wanda yake da alaka da HKI a cikin Tekun Arabian.

Kakakin sojojin kasar Burgediya Janar Yahayah Saree ya bayyana a jiya Talata kan cewa sun amfani da wani sabon makami mai linzami da suka kera a cikin gida don tarwatsa jirgin kwantena dauke da tutar kasar Liberia.

Janar Saree ya kara da cewa sabon makami mai linzamin da sojojin suka yi amfani da shi yana da karfi fancewa, sannan kuskurensa kadan ne, sannan ana iya cillashi daga nesa ya kuma sami bararsa.

Kakakin sojojin Yemen ya kara da cewa sojojin kasar zasu kara kyautata makamansu don taimakawa falasdinawa wadanda sojojin HKI suke wa kissan kiyashi a zirin Gaza. Har’ila yau don kare kasar daga ayyukan ta’addancin da sojojin kasashen Amurka da Burtraniya suke yi a kasar.

Daga karshe ya bayyana cewa wadan nan hare hare zasu ci gaba har zuwa lokacinda sojojin HKI zasu kawo karshen hare haren da suke kaiwa kan mutanen gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments