Sojojin Yemen Sun Sanar Da Kai Wa Cibiyar Sojan Sama Ta “Nivatim” Hari Sau Biyu A Cikin Sa’o’i 24

Sojojin na kasar Yemen sun sake kai hari akan sansanin sojan saman a “Nivatim” na HKI a karo na biyu a cikin sa’o’i 24. Majiyar

Sojojin na kasar Yemen sun sake kai hari akan sansanin sojan saman a “Nivatim” na HKI a karo na biyu a cikin sa’o’i 24. Majiyar sojan kasar ta Yemen ta ce wannan shi ne karo na hudu da suke kai hari akan manufofin HKI a cikin sa’o’i 24.

Kakakin sojan kasar Yemen janar Yahya Sa’ri ya fada a wata sanar wa ta tashar talabijin cewa; sojojin kasar sun kai hari da makamai masu linzami da su ka fi sauti sauri wajen kai wa sansanin na “Nivatim” hari wanda yake a cikin yankin Naqab a Falasdinu dake karkashin mamaya.

Janar Sari ya kuma kara da cewa; hare-haren da suke kai wa HKI yana a karkashin ci gaba da taya Falasdinawa fada ne da suke yi,kuma sun sami sanarar saukar makamin a inda aka harba shi.

Haka nan kuma janar Sari ya ce; sojojin na Yemen za su ci gaba da karawa kansu karfi da yardar Allah ta hanyar bunkasa makaman da suke da su domin fuskantar ‘yan sahayoniya.

A jiya Asabar ne dai sojojin na Yemen su ka sanar da cewa sun kai hare-hare biyu da jiragen sama marasa matuki akan wasu muhimman manufofi na ‘yan sahayoniya a yankin Yafa dake karkashin mamaya da kuma a yankin Asqalan dake kusa da Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments