Sojojin Yemen Sun Sake Kai Hari Kan Jirgin Ruwan Amurka Mai Dakon Jiragen Yaki Zuwa H.K.Isra’ila

Sojojin Yemen da dakarun kungiyar Ansarullah ta kasar sun sanar da sake kai hari kan jirgin ruwan Amurka kirar Eisenhower a karo na biyu a

Sojojin Yemen da dakarun kungiyar Ansarullah ta kasar sun sanar da sake kai hari kan jirgin ruwan Amurka kirar Eisenhower a karo na biyu a tekun Bahar Maliya

Rundunar sojin ruwan Yemen da dakarun kungiyar Ansarullahi ta kasar sun sanar da kai hare-hare da makamai masu linzami, da jirage marasa matuka ciki har sau shida kan jirgin na Amurka a kan hanyarsa ta tafiya haramtacciyar kasar Isra’ila ta hanyar teku.

Kakakin rundunar sojin kasar Birgediya Janar Yahya Sare’e ya bayyana cewa: Farmakin na farko ya auka wa jirgin ruwan Amurka dakon Amurka ne na “Eisenhower” da ke tafiya a shiyar arewacin tekun Bahar Maliya ta hanyar amfani da wasu makamai masu linzami na musamman da kuma jiragen sama marasa matuka ciki.

Janar Yahya Sare’e ya ce: Harin da aka kai wa jirgin ruwan Amurkan shi ne irinsa na biyu cikin sa’o’i 24 da suka gabata, yana mai jaddada cewa, farmaki na biyu ya auka wa jirgin ruwan na Amurka ne a tekun Bahar Maliya da yake dauke da tarin jiragen sama marasa matuka ciki da zai kai haramtacciyar kasar Isra’ila domin samun damar ci gaba da murkushe Falasdinawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments